Muslim Brotherhood ta sha kayi a zaben kasar Masar

Zaben kasar Masar
Image caption Kungiyar 'Yan uwa musulmi ta Muslim Botherhood dake kasar Masar tasha kayi a zaben 'yan majalisar dokokin kasar da aka gudanar ranar lahadi

Sakamakon farko na zaben 'yan Majalisu da aka gudanar ranar lahadi a kasar Masar ya tabbatar da cewa babu koda kujerar dan Majalisa daya da kungiyar nan ta 'yan uwa Musulmi wato Muslim Brotherhood, ta samu, duk kuwa da kasancewar kungiyar ce ta biyar a jerin jam'iyyun dake da mambobi a Majalisar data shude.

'Yan adawa dai sun nuna bacin ransu da sakamakon zaben

Ita ma dai Kasar Amurka tace bata ji dadin yadda sakamakon zaben ya kasance ba.

Wakilin BBC dake kasar Masar ya ce kusan kowa yayi alla-wadai da sakamakon zaben illa dai wadanda keda alaka da gwamnatin kasar ne suka nuna gamsuwa da yadda sakamakon zaben ya kasance.