Pakistan ta yi watsi da bayanan Wikileaks

Pakistan
Image caption Bayanan na Wikileaks na ci gaba da janyo cece-kuce

Kasar Pakistan ta yi watsi da damuwar da jami'an diflomasiyyar Amurka suka nuna a bayanan da shafin Wikileaks ya watsa kan makomar makaman nukiliyar ta.

Bayanan dai sun nuna cewa makaman nukiliyar kasar za su iya fadawa hannun kungiyoyin 'yan ta'adda.

Sun kuma nuna cewa kasashen Burtaniya, da Rasha da Amurka sun nuna damuwa game da tsaron makaman nukiliyar kasar ta Pakistan.

A wata takarda daban kuma, shugaba Obama na Amurka ya bayyana Pakistan a matsayin kasar da ke hana shi sukuni.

Martani

Ma'aikatar harkokin wajen Pakistan ta ce babu wani abu da ya faru da makaman nukiliyar na ta.

Wakilin BBC a Pakistan ya ce jami'an sojin kasar na kallon bayanan a matsayin wata hanya ta neman kasar ta dakatar da shirinta na nukiliya.

Har ila yau bayanan sun nuna damuwa kan ko kasar za ta iya katse hulda da kungiyoyin masu tayar da kayar baya.

A bangare guda kuma, kungiyar 'yan sanda ta kasa-da-kasa Interpol, ta nemi a bata bayanan inda mutumin da ya kirkiro shafin na Wikileaks wato Julian Assange yake zaune.