'Yan Sanda na neman mutumin da ya kirkiro Wikileaks

Julian Assange
Image caption 'Yansandan kasa da kasa na Interpol na neman mutumin daya kirkiro da shafin nan na Wikileaks ruwa a jallo

Hukumar 'yan sanda ta kasa da kasa wato Interpol, ta fitar da sammacin neman mutumin nan daya kirkiro shafin Internet na Wikileaks, Julian Assange.

Hukumar ta ce ana nemansa ne don ya amsa tambayoyi a kasar Sweden kan zargin aikata laifuffuka da suka shafi jima'i, zargin da tuni ya musanta.

A cewar hukumar, sanarwar ba tana nufin sammacin kame Julian Assange ba ne, illa dai tana nufin jama'a su tuntubi jami'an 'yan sanda ne matukar suna da bayanai game da inda shi Julian Assange yake.

Wasu bayanai na baya bayanan na sirri da shafin na Wikileaks ya fitar sun nuna cewar kasashen Amurka da Burtaniya da kuma Rasha na cikin damuwa matuka dangane da tsaron makaman nukiliyar kasar Pakistan