An gano na'urorin da ba sa aiki a injinan jirage a Australia

Jiragen Sama
Image caption Masu binciken lafiyar jirage a Kasar Australia sun gano wasu na'urorin da basa aiki a wasu injinan jiragen saman kasar

Masu binciken tsaron lafiyar harkokin zirga zirgar jiragen sama na kasar Australiya sun ce sun gano wasu na'urori da basa aiki a wasu injinan jiragen sama kirar Jet da aka sanyawa jirgin saman fasinjoji mafi grima a duniya, wato Airbus A-380.

Sun bayyana cewa akwai wasu muhimman batutu na tsaron lafiya, daka iya haifar da lalacewar injin din jirgin.

A watan daya gabata ne kamfanin zirga zirgar jiragen sama na Australiya, Qantas, ya dakatar da tashin daukacin jiragensa bayan lalacewar injin din daya daga cikin jiragen saman kamfanin lokacin daya tashi, lamarin daya sa tilas jirgin yayi saukar gaggawa.