Ghana ta nemi Libya ta sako 'yan kasarta

Gwamnatin kasar Ghana ta ce tana iyakacin kokarinta don ganin an sako wasu 'yan kasar sama da casa'in dake tsare a kurkukun kasar Libya.

Karamin ministan harkokin wajen kasar Ghanan wato Mr. Chris Kpodo shi ne ya fadi hakan a gaban majalisar dokokin kasar a yau, Alhamis.

Mr Kpodo ya ce jami'an tsaron kasar Libya sun yi zargin cewa sun cafke 'yan kasar Ghana su casa'in da bakwai ne bayanda suka yi satar shiga wasu jiragen ruwa a kokarinda suke yi na tsallakawa zuwa wasu kasashen Turai daga kasar ta Libya.

A duk shekara 'yan Afrika da dama ne ke kokarin ketara teku, domin shiga nahiyar Turai, inda da dama ke rasa rayukansu.