An umurci gwamnan Kano ya nada kantomomi

A yau wata babbar kotu a jahar Kano ta umarci gwamnan jahar da kwamishinan shari'a da su nada mutanenda za su riki ragamar kananan hukumomin jahar 44 har zuwa lokacinda hukumar zaben jahar za ta iya gudanar da zabe nan da dan lokaci.

Mai shari'a Muhammad Sadi Mato ya kuma umarci hukumar zaben jihar da ta shirya zaben kananan hukumomi, cikin mafi karancin lokacin iyawarta.

Wannan hukuncin dai ya biyo bayan karar da mataimakin shugaban karamar hukumar Rimin Gado Muhuyi Magaji ya shigar ne yana neman kotu ta yi fassara kan sashi na Hamsin da Takwas karamin sashi na daya wanda ya baiwa gwamna da majalisa damar nada shugabannin kananan hukumomi, wanda a cewar mai karar, ta ci karo da sashi na Bakwai karamin sashi na daya a kundin tsarin mulkin Nigeria na shekarar 1999.