Nigeria za ta tuhumi Dick Cheney

Dick Cheney
Image caption Dick Cheney

Hukumar yaki da yiwa tattalin arziki zagon kasa a Nigeria, ta ce za ta gurfanar da tsohon mataimakin shugaban kasar Amurka, Dick Cheney a gaban shari'a a Nigeria.

Hukumar ta bayyana haka ne a yayin da ta ke ci gaba da bincike akan abun kunyar nan na cin hanci da rashawa da ya shafi kamfanin Halliburton.

Kakakin Hukumar ta EFCC a Nigeria, Femi Babafemi, ya bayyana cewar hukumar ta shirya shigar da karar tsohon mataimakin shugaban na Amurka a makon gobe.

A tsakanin shekarun 1995 zuwa 2000, tsohon mataimakin shugaban Amurkar, Dick Cheney, shine ya shugabancin kamfanin na Halliburton.