An sabunta: 3 ga Disamba, 2010 - An wallafa a 12:57 GMT

Matsanancin Halin Rayuwa: Zai bayyana bambancin rayuwa a sassan duniya

Matsanancin Halin Rayuwa wani sabon shiri ne da za'a watsa ta gidan rediyo da talabijin da kuma intanet na BBC, wanda zai duba banbance-banbancen da ke tsakanin al'umma.

Nan da 'yan watanni masu zuwa, wakilan BBC za su yi karin haske kan wasu abubuwa takwas da suka banbanta yadda muke rayuwa.

A shirin farko, wanda zai duba yanayin zafi da sanyi, wakilin BBC Adam Mynott zai ziyarci kauyen Oymyakon na kasar Rasha, inda aka ce shi ne yafi kowanne yanki tsananin sanyi a duniya.

A garin Omyakon, matsakaicin yanayi a watan Janairu shi ne -46 digiri a ma'aunin salshiyos. Shi dai yankin na da arzikin gwal da kuma daiman - kuma a yanzu Rasha na daya daga cikin kasashen da suka fi samar da daiman a duniya.

BBC navigation

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.