Gbagbo ne ya lashe zaben Ivory Coast

Gbagbo ne ya lashe zaben Ivory Coast
Image caption Da farko hukumar zabe ta ce Alassane Ouattara ne ya yi nasara.

Majalisar tsarin mulkin Ivory Coast ta sanar da shugaban kasar Laurent Gbagbo a matsayin wanda ya lashe zaben kasar, bayanda tun farko hukumar zabe ta ce Alassane Ouattara ne ya yi nasara.

Shugaban Majalisar Paul Yao N'Dre, wanda na hannun damar shugaban kasar ne, ya ce Mista Gbagbo ya lashe kashi 51 na kuri'un da aka kada. Ya kara da cewa Majalisar, wacce ke da alhakin amince wa da sakamakon zaben, ta soke zaben yankuna 7 na Arewacin kasar - inda jagoran 'yan adawa Alassane Ouattara ya samu yawancin kuri'unsa.

A ranar Alhamis Hukumar zaben kasar ta sanar da Mr Ouattara a matsayin wanda ya lashe zaben, sai dai Majalisar tsarin mulki ta yi watsi da sanarwar.

Daga bisani sojojin kasar sun rufe kan iyakokin kasar ta kasa da ta ruwa, sannan suka dakatar da kafafen yada labarai na kasashen waje.