Rikicin siyasa a Nijeriya. Ina mafita?

Parfesa Attahiru Jega, shugaban hukumar zabe
Image caption Parfesa Attahiru Jega, shugaban hukumar zabe

A yayinda zabubbukan Nigeriya ke karatowa, wani batu dake haddasa fargaba a zukatan yawancin 'yan kasar shi ne matsalar tsaro a lokacin zabe.

Wani abun damuwa kuma shi ne yadda a baya- bayan nan hukumomin tsaron kasar su ka kama makamai a gabar ruwan Lagos, wanda wasu ke ganin bai rasa nasaba da yadda wasu ke daukar zabukan na badi, 'ko a mutu ko a yi rai'.

Tashe tashen hankula a lokacin zabubbuka a Najeriya ba sabon abu ba ne.

Rayuka da dukiya na salwanta a irin wadannan rikice-rikicen siyasa.

Ko a yau din nan sai da aka sami hatsaniyar siyasar a tashar Magarya da ke kusa da garin Kumo a jahar Gombe.

Daga cikin bakin da muka gayyato a shirin sun hada da;