Haiti na cigaba da fama da annobar kwalara

Annobar kwalara a Haiti
Image caption Kimanin mutane dubu dari shida da hamsin ne zasu iya kamuwa da cutar kwalara nan da watanni shida masu zuwa.

Majalisar Dinkin Duniya tayi gargadin cewa annobar cutar kwalara data bulla a kasar Haiti ka iya shafar mutane fiye da yadda ake zato.

Babban Sakataren Majalisar Dinkin Duniya Ban Ki-moon, ya ce jami'an kiwon lafiya sun kiyasta cewa kimanin mutane dubu dari shida da hamsin ne zasu iya kamuwa da cutar nan da watanni shida.

Ya kara da cewa Majalisar Dinkin Duniyar tayi amannar cewa adadin mutanen da suka mutu ka iya nunkawa har sau biyu na yawan adadin mutanen da tun da farko jam'ian suka bayyana cewa sun mutu.

Ya ce kamar yadda aka sani annobar ta yadu zuwa dukkanin sassan kasar da kuma Port-au-Prince babban birnin kasar

Rahoton ma'aikatar lafiya ya nuna cewa adadin mutanen da suka mutu sun zarta mutum dubu daya da dari takwas.