Ana saka rai da zuwan Thabo Mbeki Ivory Coast

Ana saka ran isar tsohon shugaban kasar Afirka ta kudu Thabo Mbeki Ivory Coast domin yunkurin samar da maslaha ga takaddamar da aka samu a zaben shugabancin kasar.

A yayin da Ivory Coast ke kokarin ganin wanda zai warware takaddamar da ta far wa kasar, ana ci gaba da tofa albarkacin baki dangane da halartar Thabo Mbeki.

Mr. Mbeki dai a lokacin da yake shugaban kasar Afirka ta kudu, ya taba taimakawa wajen ganin an cimma yarjejeniyar zaman lafiya a Ivory Coast.

A wancan lokacin da yake kokarin ganin an sasanta, 'yan adawa na masa kallon cewa ya na da kusanci da Shugaba Laurent Gbagbo.

Sai dai kuma, ko ma ta halin kaka, a yanzu dai kam basu da wani zabi da ya yi musu saura.

Alasanne Watara da magoya bayansa dai sun amince da cewa sune suke da nasara.

Kuma Majalisar dinkin duniya ta amince da cewa an kammala kirga dukkan kuri'un.

Shi dai Shugaba Gbagbo dai ya dage ne akan cewa wadansu kuri'un da aka kada daga arewacin kasar sun saba da demokradiyya, don haka dole a soke su, lamarin da ya janyo soke dubban kuri'un da Mista Watara ya samu.

To fargabar dai itace idan har a wannan karon ma Mr. Mbeki bai yi nasarar daidaitawa ba, to akwai yiwuwar masu fafutuka a Arewacin kasar na iya sake dauko makamansu, domin nuna rashin amincewa.