Shugaba Gbagbo na shirin rantsar da kansa

Shugaba Laurent Gbagbo na Ivory Coast
Image caption Shugaba Laurent Gbagbo na Ivory Coast na shirye shiryen rantsar da kansa a matsayin wanda ya lashe zaben shugabankasar da aka gudanar ranar lahadi

Gidan talbijin na gwamnati a Ivory Coast ya ce idan an jima a yau asabar za'a rantsar da shugaban kasar mai ci yanzu, Laurent Gbagbo karo na biyu, duk kuwa da cewa abokin karawarsa Alassane Wattara, ya bayyana kansa a matsayin wanda ya lashe zaben da aka fafata a ranar lahadi.

Mr. Gbagbo na samun goyon bayan manyan hafsoshin sojojin kasar, yayin da shi kuma Mr. Wattara ke samun goyon bayan Majalisar Dinkin Duniya da kungiyar kasashen yammacin Afrika, ECOWAS, da kuma kasar Faransa wacce ta mulki kasar a shekarun baya.

Tunda farko wakilin Majalisar Dinkin Duniya na musamman a kasar Ivory Coast, Choi Young-jin, ya shaidawa BBC cewa cewa su dai sun san cewa babu tantama game da wanda ya lashe zaben.