Shugabannin kananan hukumomin Kano sun aje aiki

A Jihar Kano dake Najeriya, a karshen makon nan ne wa'adin mulki shugabannin kananan hukumomin na jihar ya zo karshe.

Shugabannin dai sun shafe shekaru uku a kan karagar mulki.

Sai dai a yayin da shugabannin ke ajiye ayyukan su, wasu cewa suke yi basu gamsu da yadda shugabannin kananan hukumomin suka tafiyar da al'amuran jagoranci a Jihar ba.

Amma kuma a daya bangaren, su shugabannin kananan hukumomin, cewa su ke yi, idan har ba a gode musu ba, to kuwa ba'a yi musu Allah Wadai ba.