Mutane 3 sun mutu a araganma a Maiduguri

Boko haram

A Najeriya, rahotanni sun ce mutane ukku ne suka mutu a wata musayar wuta da aka yi tsakanin jami'an tsaro da wasu mutane da ake zargin 'yan Boko Haram ne a birnin Maiduguri.

Kakakin rundunar 'yan sandan Jihar Bornon, ASP Lawal Abdullahi ya tabbatarwa da BBC cewa jami'an tsaro sun rinjayi wadanda suka kai harin.

ASP Lawal Abdullahi ya bayyana cewa suna samun nasara a matakan da suke dauka na ci gaba da kokarin ganin an kawo karshen matsalar Boko Haram a Jihar Borno, musamman a Birnin Maiduguri.

Mazauna unguwannin Budum da Kofa Biyu da kuma State Low Cost, inda a baya aka bayyana cewa daga nan rikicin Boko Haram ya faro, sun ba da rahoton jin karar bindigogi.

A 'yan watannin da suka gabata dai wasu da ake zargin 'yan Boko Haram ne, sun hallaka mutane da dama a birnin na Maiduguri da ma wasu sassa na arewacin Najeriya.