A Nijar Jamiyyar PLD ta ce za ta karfafawa mata gwuiwa

A jamhuriyar Nijar, shugaban jam'iyyar PLD Mamaki Alhaji Abubakar Ganda Sa'idu, ya ce jam'iyyarsa za ta fi mayar da hankali wajen kyautata rayuwar mata da kananan yara idan har ta samu wakilci, a kananan hukumomi da majalisar dokokin kasar.

Shugaban Jam'iyyar dai ya bayyana cewa a kananan hukumomi ne ko a majalisar dokoki ake girka demokradiyya.

Shugaban ya fadi haka ne a wurin wani taro da jam'iyyar ta shirya a Birnin Yamai domin wayar da kan magoya bayanta dangane da shirye-shiryen zabubuka masu zuwa.

Jam'iyyar PLD dai na daga cikin sababbin jam'iyun da suka bullo a bana, wadda akasarin mambobinta, mata ne.