Sojin Spain sun kwace ikon harkokin jiragen sama

Jiragen sama a kasar Japan
Image caption Sojoji a kasar Japan sun kwace ikon gudanar da harkokin zirga zirgar jiragen saman kasar bayan yajin aikin da ma'aikatan jiragen suka yi

Sojojin kasar Spain sun karbe ikon harkokin tafiyar da zirga zirgar jiragen sama a kasar sakamakon wani yajin aikin da ma'aikata fararen hula suka shiga.

Hakan dai ya tilasta rufe manyan filayen jiragen sama dake kasar bayan da ma'aikatan suka fara yajin aikin, don nuna rashin jin dadinsu game da yanayin aiki.

Ministan ma'aikatar sufuri Yose Blanco ya ce gwamnatin kasar na daukar dukkanin matakan da suka kamata na ganin an ci gaba da zirga zirgar jiragen sama.

Ministan yace yana baiwa jama'a hakuri wadanda basu samu damar yin tafiye tafiye ba sakamakon yajin aikin da ma'aikatan dake kula da zirga zirgar jiragen sama suka shiga.