'Yan cirani na cigaba da shiga kasar Yemen

'Yan cirani
Image caption Ana ci ga da samun karuwar baki 'yan kasashen Afrika da ke zuwa cirani wadanda aka koro su daga kasar Saudiya zuwa kasar Yemen

Ma'aikatan agaji sun ce ana ci ga da samun karuwar baki 'yan kasashen Afrika da ke zuwa cirani wadanda aka koro su daga kasar Saudiya zuwa kasar Yemen dake makwabataka da kasar, inda daga bisani suke mutuwa a can.

Kungiyar kasa da kasa dake sa ido akan masu yawon ci rani, ta ce rahotannin data samu daga wasu kungiyoyin da take mu'amala sun bayyana cewa mutane talatin ne suka mutu a kan iyakokin Yemen a 'yan makwannin nan.

Kungiyar ta kara da cewa kimanin 'yan kasashen Afrika dubu biyu ne ke cikin wani mawuyacin hali na rashin kudade, da rashin abinci da kuma ruwan sha a garin Haradh dake kasar Yemen, wadanda kuma akasarinsu sun fito ne daga kasashen Somaliya, da Habasha da kuma kasar Masar.