Tabo ya binne gidaje da dama a Colombia

A yayinda kasar Colombia ke fama da matsalar ambaliyar ruwa da kuma ruwan sama da ake ci gaba da tsugawa, kimanin gidaje hamsin ne ake tunani tabo ya rufe a garin Bello, dake wajen Madellin.

Ana kuma tunanin mutane da dama sun rasu a wannan masifar da ta afka musu.

Ambaliyar ruwa dai ta mamaye mafi yawan garuruwa a kasar, lamarin da ya salwantar da muhallin dubban al'umma.

Sai dai a garin Bello dake wajen Madellin, ruwan ya yi sanadiyar kwararar tabo daga wani tsauni wanda ya lullube gidaje.

Mazauna yankin sun yi ta tono da hannayensu domin kokarin ceto wadanda tabon ya binne.

Shugaba Juan Manuel Santos dai ya fara tunanin bayyana abinda ke faruwa a kasar a matsayin lamarin da ke matukar bukatar a kai masa dauki, musamman ma a yayinda ake ci gaba da tsuga ruwa kamar da bakin kwarya a kasar.