PDP ta ce za ta tantance 'yan takara a Jam'iyyar

A Nigeria jamiyyar PDP mai mulkin kasar ta ce za ta tantance duk 'yan jam'iyar masu sha'awar tsayawa takara a zabe mai zuwa.

Jam'iyyar dai ta bayyana cewa za ta yi wannan tantancewar ne domin tabbatar da cewa an yi biyayya ga dokokin kundin tsarin mulki da na jam'iyar.

Hakan a cewar jam'iyar ya shafi dukkanin mukamai, kuma za ta yi shi ne domin ganin ba'a tsayar da baragurbin 'yan takara ba.

Sai dai wasu 'yan jam'iyar na nuna fargabar cewa za'a iya amfani da tantacewar don ta dakatar da wasu 'yan takara.