An ba Biritaniya sammacin kama shugaban Wikileaks

Julian Assange
Image caption Ana neman yi masa kofar raggo

Mahukunta a fannin shari'a a kashen duniya sun kara matsa lamba kan mai shafin intanet din nan na Wikileaks, Julian Assange, wanda tona wasu bayanan sirrin da ya yi ya hasala Amurka da wasu kasashe.

Atoni Janar na Amurka, Eric Holder, ya bayyana cewa ana neman dokar da za ta ba da damar gurfanar da shi a kan fallasar da ya yi.

Gwamnatin Birtaniya ta sami wata takaddar sammaci daga kasar Sweden ta kama Mr. Assange.

Wakilin BBC y ace, “Sanin cewa yanzu haka yana nan Birtaniya, tuni aka mika wa 'yan sanda takaddar samacin kama shi duk inda ya shiga a kasar.

Lauyan Mr Assange ya kwatanta matakin kamashin a matsayin na siyasa wanda ya saba dokokin Turai kan tasa keyar mutum zuwa wata kasa.