Kotu ta samu Continental da laifi

jirgin Concorde
Image caption jirgin saman Concorde yana cin wuta lokacin da ya fadi

Wata kotu a Faransa ta dora alhakin faduwar jirgin saman nan na Concorde a kan kamfanin jirgin sama na Continental Airlines dake Amurka.

Masu gudanar da bincike kan faduwar jiragen sama sun yanke hukunci tun shekaru da suka gabata cewa, wani karfe ne ya fado daga jirgin saman Continental DC-10, wanda ya haddasa faduwar jirgin, wanda ya halaka mutane sama dari.

Sun yi imanin cewa wannan karfe ne ya fasa daya daga cikin tayoyin jirgin na Concorde, wanda ya tarwatsa robar da ta watsu zuwa tankin man jirgin.

An dai samu daya daga cikin makanikan jirgin da laifin yunkurin kisan kai ba da nufi ba, an kuma yanke masa hukuncin daurin gyara hali na