Shugabannin ECOWAS na taro kan rikicin Ivory Coast

Image caption ECOWAS CEDEAO

A Najeriya, Shugabannin kungiyar habaka tattalin arzikin kasashen Yammacin Afrika wato ECOWAS ko CEDEAO suna gudanar da wani taron gaggawa a Abuja babban birnin kasar, game da rikicin kasar Ivory Coast.

Shugabannin suna duba yiwuwar warware sarkakiyar da aka samu a siyasar Ivory Coast, sakamakon ayyana kansu da 'yan takarar shugabancin kasar guda biyu suka yi a matsayin shugaban kasa.

Wannan ya biyo bayan zagaye na biyu na zaben shugaban kasar da aka gudanar.

A yanzu dai duka mutanen biyu, wato Laurent Gbagbo da Alassane Ouattara sun fara yunkurin kafa gwamnati.

Majalisar dinkin duniya da kasar Faransa da Tarayyar Afrika sun yi kira ga Mista Gbagbo da yayi murabus, amma kawo yanzu bai nuna alamar yin hakan ba.

Shugaba Gbagbo ya tura wata tawagar kamun kafa zuwa Ghana ranar Litinin inda tawagar ta gana da Shugaba John Atta Mills.

Karanci da Tsadadar Abinci

Bayanai sun nuna cewa a yanzu ana fama da karancin kayan masarufi a kasar Ivory Coast, yayinda farashin wasu kayayyakin ciki har da Cocoa ya tashi, yayinda ake ci gaba da fama da kiki-kakan siyasa.

Shaguna da dama sun rufe saboda karancin kayayyaki da suka hadar da nama, kifi, fetur, iskar gas din girki da sauransu.

Kasar ivory Coast dai ita ce kasar da ta fi kowacce samar da Cocoa a duniya.

Shugabannin kasashen yammacin Africa karkashin lemar kungiyar habaka tattalin arzikin yammacin Afrikan suna gudanar da taron gaggawar ne a Abuja, a daidai lokacin da sauran shugabannin kasashen duniya ke kira ga shugaba Gbagbo da ya mika mulki.

Sun ce jagoran 'yan adawa Alassane Ouattara ne ya lashe zaben da aka gudanar ranar 28 ga watan Nuwamban da ya gabata.

Zaman dar-dar

Yayinda ake ci gaba da zaman dar-dar a kasar, majalisar dinkin duniya ta fara janye ma'aikatanta da aikinsu bai zama dole ba daga kasar.

A ranar Litinin mai shiga tsakani na tarayyar turai, tsohon shugaban Afrika ta Kudu Thabo Mbeki ya bar kasar ta Ivory Coast bayan tattaunawar da ya gudanar da bangarorin biyu ya kasa kawo karshen rikicin.

Kasar ta Ivory Coast dai ta rabu biyu tun shekarar 2002 sakamakon yakin basasa.

A baya dai ana ganin kasar a matsayin watta aljannar zaman lafiya a yammacin Afrika.

Zaben shugabancin kasar na bana dai ya zo a karshen tattaunawar zaman lafiyar da aka yi tsakanin gwamnati da 'yan tawaye.