Faransa ta nemi Gbagbo ya sauka

Faransa ta nemi Gbagbo ya sauka daga kan mulki
Image caption Kasar ta Ivory Coast dade tana fama da rikicin siyasa

Shugaban kasar Faransa, Nicolas Sarkozy, ya sake yin kira ga takwaransa na kasar Ivory Coast, Laurent Gbagbo da ya sauka daga kan mulki, sakamakon zaben da ake takaddama a kansa.

A Makon jiya, Mr Sarkozy ya ce ya kamata Mr. Gbagbo ya mutunta abin da 'yan kasar ke so, bayan zaben da Faransa, da Majalisar Dinkin Duniya da wasu kungiyoyin kasashen waje suka ce abokin hamayyarsa Alassane Qatara ne ya lashe shi.

Mr. Sarkozy ya ce: "Tilas ne yanzu ya mika shugabanci ga wanda jama'a suka zaba. Faransa ba ta san yin katsalandan a harkokin cikin gidan Ivory Coast".

A karshen makon da ya gabata ne duka mutanen biyu Laurent Gbagbo da Alassane Qatara suka rantsar da kansu a matsayin shugaban kasar.

Sakamakon ziyarar Thabo Mbeki

Ana sa ran tsohon shugaban kasar Afrika ta Kudu Thabo Mbeki, zai gabatar da matsayinsa bayan kammala ziyarar sasantawa da ya kai kasar Ivory Coast domin kokarin warware rikicin siyasar kasar.

Zai yi tattauna wa ta karshe tare da Laurent Gbagbo, wanda shi ne shugaban kasar tun shekaru goma da suka gabata.

Kuma a cewar hukumar zaben kasar wadda ke samun goyon bayan Majalisar Dinkin Duniya, ta ce bai ci zaben ba.

A yanzu dai an bude iyakokin kasar, to amma Majalisar Dinkin Duniya da wasu gwamnatoci, na shawartar mutanen kasarsu da cewa kada su kuskura su je kasar ta Ivory Coast, saboda yiwuwar barkewar tashin hankali.