Majalisar Najeriya ta ne dalilin shirin cin bashi

Tutar Najeriya
Image caption Majalisa na tsohon sake jefa kasar cikin sabon bashi

A yau ne ministan kudi na Najeriya, Dokta Olusegun Aganga, ya yi bayani ga kwamitin hadin gwiwa na kudi da kuma lura da karbar rance na Majalisar Wakilai ta kasar.

Bayanin dangane da bashin dala biliyan ukku ne da miliyan dari bakwai da gwamnatin kasar ke shirin karbowa daga cibiyoyin kudi na kasa-da-kasa.

Ministan ya bayyana cewa za a yi amfani da bashin ne wurin samar da ababen more rayuwa ga 'yan Najeriya, ciki har da wutar lantarki.

Shirin karbo bashin dai na zuwa ne a daidai lokacinda 'yan Najeriya ke nuna damuwa a kan yiwuwar sake jefa kasar cikin tarkon bashinda ba a jima da fitowa ba.