An fara rigakafin sankarau a Nijar

A jamhuriyar Nijar, yau ne hukumomin kiwon lafiya na kasar suka kaddamar da wani shiri na yi ma al'umma rigakafin cutar Sankarau.

Kimanin mutane miliyan ukune hukumomin ke sa ran za su ci moriyar shirin.

Sai dai a matakin farko, aikin zai kai ga jihohin Yamai da Doso ne, kafin daga bisani ya kai ga sauran yankunan kasar.

Hukumar lafiya ta duniya WHO ko OMS tare da hadin gwiwar wasu masu hannu da shuni ne ke taimakawa shirin, wanda zai kai ga wasu kasashe makwabtan Nijar din irin su Mali, da Burkina Faso.