Sweden ta nemi Julian Assange ya amsa wasu tambayoyi

Mako guda bayan da shafin yanar gizo na Wikileaks ya bankado wasu bayanan sirri na abin kunya ga gwamnatin Amurka, ana ci gaba da tsaurara mastin lamba game da shafin da kuma wanda ya kirkiro shi wato Julian Assange.

Lawyoyin Mr. Assange dai sun tabbatar da cewa a shirye yake da ya gana da 'yan sandan Birtaniya, wadanda aka mikawa takardar sammacin chafke shi.

Ana neman sa ne domin ya amsa wasu tambayoyi a kasar Sweden dangane da wani zargi da ake masa na yin fyade, lamarin da shi ya musanta.

Duk da dai cewa ba'a gurfanar da Julian Assange din a gaban kotu ba, ana dai neman sa ne domin amsa wadansu tambayoyi game da zargin.

Wani Lawyansa dake Birtaniya, Mark Stevens ya tabbatar da cewa gwamnatin Sweden ta nemi da a mika mata shi.

Sai dai ya ce suna shirin ganawa da 'yan sandan Birtaniya bisa radin kansu.

Ana saka ran cewa kwana daya bayan bayyanar Mr. Assange din a gaban 'yan sandan, za'a gurfanar da shi a gaban kuliya.

Bayanan da shafin Wikileaks din ya bankado na baya bayan nan, sun yi karin haske ne akan alakar kungiyar tsaro ta Nato da Russia.

Bayanan na nuni da cewa baicin yunkurin da suke yi a fili na ganin sun baiwa juna hadin kai, Amurka da sauran kawayen ta na kasashen yammaci kamar irinsu Birtaniya na ta shirin yanda zasu yi wajen kare 'yan cin wasu kasashen yankin Baltic kamar irinsu Estonia da Latvia da ma Lithuania daga duk wani cin zarafi da suke fuskanta daga Russia.