Morgan Tsvangarai ya ce sai an yi gyara kafin zabe

Fira Ministan Zimbabwe, Morgan Tsvangirai ya ce babu yanda za'a yi a iya yin sabbin zabubuka a kasar idan har ba a yi sauye- sauye ba.

Mista Tsvangarai dai ya ce daga cikin sauyin da ya kamata a yi, har da amincewa akan sabon kundin tsarin mulkin kasar

A wata hira da ya yi da kamfanain dilanci labarai na reuters Mista Tsvangirai ya ce gudanar da zabe kafin kada kuri'ar raba gadama wato rafarandum akan wasu mauhimamman abubuwa zai iya sake janyo tashe tashen hankula, kamar wanda suka faru a lokacin zaben shekarar 2008.

Shi dai shugaban kasar ta Zimbabwe wato Robert Mugabe, wanda suke raba iko tare da Mista Tsvangarai ya nemi da a yi zabe ne a watan Yunin badi.