Kasashen Afirka ta yamma sun yanke alaka da Ivory Coast

Shugabannin kasashen Afirka ta Yamma sun ba da sanarwar dakatar da kasar Ivory Coast daga dukkan harkokin su har sai Laurent Gbagbo ya mika ragamar ikon kasar ga Alassane Ouattara.

Alassane Ouattara dai shine wanda suka ce sun yi amannar cewa shi ne ya lashe zaben da aka gudanar a kasar.

A jawabin bayan taron da suka fitar, bayan kammala wani taron koli na gaggawa a Abuja, shugabannin sun ce ba za su yi amfani da karfin soji wajen tilastawa Mista Gbagbo ya amsa bukatar su ba.

Sai dai sun bayyana cewa suna goyon bayan duk wani mataki da hukumomi na kasa-da- kasa da sauran kasashen duniya za su dauka a kan kasar Ivory Coast.