An kama Julian Assange

Shafin Wikileaks
Image caption Shafin Wikileaks

'Yan sandan Burtaniya sun kame mutumin nan da ya assasa shafin intanet din nan mai kwarmata bayanai na Wikkileaks, Julian Assange.

Assange mai shekaru 39, ya musanta zargin da ake yi masa na yiwa wasu mata biyu fyade a kasar Sweden.

Hukumomin 'yan sandan London a Scotland yard sun ce, sun kame Mista Assange ne ta hanyar amfani da wata takardar sammaci ta turai a lokacin da suka gayyace shi zuwa ofishinsu.

Zai dai bayyana a gaban kotun Majistare da ke Westminster nan gaba.

Zargi

Hukumomin kasar Sweden ne ke zargin Mr Assange da laifin fyade, da tilastawa da kuma cin zarafin wasu mata a cikin watan Agustan shekarar 2010.

'Yan sanda sun tuntubi lauyansa, Mark Stephens a daren ranar Litinin bayan sun samu sammaci daga hukumomin kasar Sweden.

Mista Stephens ya ce mutumin da yake karewa yana son ya samu karin bayani a kan zargin da ake yi masa domin ya wanke kansa.

Ya kuma kara da cewa Mr Assange ya yi ta kokarin ganawa da mai shigar da kara na kasar ta Sweden ta hanyoyi da dama domin samun karin bayni a kan tuhumar da ake yi masa.

Ana dai ta sukar Mr Assange a tsawon mako gudan da ya gabata saboda irin bankade-bankaden sirrika da shafinsa na Wikileaks ke yi.

A ranar Litinin din da ta gabata, sakataren harkokin wajen Burtaniya William Hague, ya soki shafin saboda wallafa bayanai a kan wasu wurare masu matukar muhimmanci ta fannin tsaro a sassa daban-daban na duniya, ciki har da Burtaniya .

Sakataren harkokin wajen ya ce, wallafa wadannan bayanan ka iya baiwa 'yan ta'adda damar kai wa wadannan wuraren hari.