'Yan sandan Jihar Borno a Najeriya sun kama mutum takwas

Rundunar 'Yan sandan Jihar Borno dake Arewacin Najeriya ta bayyana nasarar cafke mutane takwas da take zargi da kaddamar da hare-hare a wasu unguwanni dake cikin birnin Maiduguri a daren asabar din da ta gabata.

Rundunar ta bayyana kame motoci uku da ake kyautata zaton anyi amfani da su wajen kai wadannan hare-hare.

Kimanin mutane uku ne ciki har da wani yaro dan shakera biyar suka rasa rayukan su a yayin da shida suka samu munanan raunuka sakamkon musayar wutar da aka yi tsakanin 'yan bindigar da jami'an tsaro.

Wannan lamarin dai ya kara jefa mazauna birnin Maiduguri cikin zullumi da fargaba.