Na'urorin rajista sun fara isa Najeriya

Parfesa Attahiru Jega, shugaban INEC
Image caption Parfesa Attahiru Jega, shugaban INEC

Hukumar zabe mai zaman kanta a Najeriya, INEC, ta ce kashin farko na naurorin yin rajistar masu zabe ya isa kasar.

Hukumar ta ce, ba zata bata lokaci ba wajen fara horar da jami'an da za su yi aikin rajistar masu zaben a dukan jihohin kasar.

Kimanin sati biyu kenan da INEC ta bayyana tsarin aikace-aikacenta, inda ta ce tana sa ran yin rajistar masu zabe tsakanin 15 zuwa 29 ga watan Janairun shekara mai zuwa.

Hukumar zaben dai ta bayyana cewa, muddin ba a sabunta rajistar masu zaben ba, to zai yi wuya a samu ingantaccen zabe a kasar.