A Najeriya an hana korarrun 'yan majalisa shiga majalisar

A Najeriya,majalisar wakilan kasar ta ce ba za ta bari 'yan majalisar da ta dakatar su halarci zaman majalisa ba, duk da hukuncin da wata kotu dake Abuja ta yanke wadda ta umarce ta da ta amince da su.

Majalisar ta ce ba ta yarda cewa wata kotu ta yanke hukunci kan batun ba, domin kuwa ba ta aike mata da hukuncin ba.

A jiya ne dai 'yan majalisar su biyar su ka yi yunkurin shiga majalisar, sai dai an jibge jami'an tsaro a kofar majalisar, abin da su ka ce wani yunkuri ne na hana su zama a majalisar.

A watan Yuni ne dai 'yan majalisar da aka dakatar suka zargi kakakin majalisar da wawure miliyoyin kudade, abin da ya jawo zazzafar mahawara da tasa aka dakatar da su.