Majalisar dokokin Plateau ta kasa zama

Gwamnan jahar Plateau, Jonah Jang
Image caption Gwamnan jahar Plateau, Jonah Jang

Wasu dimbin matasa sun yiwa majalisar dokokin jahar Plateau kawanya, inda suka hana 'yan majalisar zamansu na yau.

Matasan masu zanga zanga sun yi cincirindo a harabar majalisar dokokin, bayan da wasu bayanai sun yi zargin cewa, 'yan majalisar suna yunkurin tsige gwamnan jihar, Jonah Jang, kuma zasu yi zama yau a kan wannan batu.

Ana zargin gwamnan na Plateau da tura wadannan matasa domin su kawo cikas ga zaman majalisar. To amma gwamnan ya musanta zargin.

A 'yan shekarun nan jahar ta Plateau tayi fama da rikice rikice masu nasaba da siyasa da addini da kuma kabilanci, wadanda suka janyo hasarar dimbin rayuka da dukiya.