Gwamnan babban bakin Nigeria ya kafe kan bakarsa

Gwamnan babban bankin Nigeria
Image caption Malam Sanusi Lamido Sanusi

A Najeriya, shugaban babban bankin kasar, Malam Sanusi Lamido Sanusi, ya Gurfana a gaba kwamitin majalisar wakilan kasar mai kula da kasafin kudi.

Yan majalisar wakilai, sun masa tambayoyi game da kalamanda yayi na cewa ana kashewa majalisar kudi fiye da kima.

Gwamnan babban bankin ya tsaya kan matsayinsa na cewa yan majalisar na kashe kashi ashirin da biyar cikin dari na kudadenda ake kashewa daga kasafin kudin kasar.

Yan majalisar dai sun bayyana cewa yayi kuskure, kuma akwai bukatar ya tantance abu kafin ya bayyana shi.