An kasa cimma yarjejeniya a gabas ta tsakiya

Shugaban Falasdinawa Mahmoud Abbas ya ce an kasa cimma matsaya a tattaunawar sulhu bayan Isra'ila ta ki daina gina matsugunan Yahudawa a yankin Falasdinawa.

Kalamin Abbas ya biyo bayan yunkurin da gwamnatin Amurka ke ci gaba da yi ne na ganin an sake komawa teburin tattaunawa a tsakanin Isra'ila da Falasdinu, lamarin da ya kusa kaiwa ga makura.

Mista Abbas ya dakatar da tattaunawa tsakaninsa da Isra'ila a watan Satumba, bayan wata goman da Isra'ila ta diba na dakatar da gina matsugunai a gabar yammacin kogin Jordan ya cika.

Amurka ta sha alwashin dawo da bangarorin biyu teburin sulhu.

An dai dawo tattaunawar sulhu ne a birnin Washington a watan Satumba bayan da bangarorin biyu su ka dakatar da tattaunawa kusan shekaru biyu, amma makonni biyu da dawowa kan teburin sulhun, tattaunawar ta kara wargajewa.

Da yake jawabi a lokacin da ya kai ziyara birnin Athens, Shugaba Abbas ya ce tattaunawa tsakanin Falasdinu da Isra'ila na cikin rashin tabbas.

A ranar Talata Washington ta bayyana cewa ta kasa cimma matsaya tsakanin ta da Isra'ila game da gina sababbin matsugunai.

Ofishin Pira Ministan Isra'ila Benjamin Netanyahu ya fito da wata sanarwar da ta ce Isra'ila a shirya take ta dawo teburin sulhu.

Kokarin gwamnatin Amurka

Wadansu masu sharhi akan al'amura dai na ganin hanyar da gwamnatin Obama ke bullowa al'amuran sun dogara ne akan wadansu kura kurai.

Wadansu sun kalubalanci kasancewar dakatar da gina matsugunnan yahudawa 'yan kama wuri zauna sharadi a yarjejeniyar zaman lafiyar da ake son cimmawa.

Wasu kuma sun ce dakatar da gine ginen wani abu ne da ya zama lallai, tun da dai batun ya raja'a ne akan gine ginen matsugunnan yahudawa 'yan kama wuri zauna da Israela ke yi.

Abin dai da yake a bayyane shi ne wasu na ganin zai fi kyau shugaba Obama ya kai ziyara Isara'ila domin yin magana gaba da gaba da al'umar yankin kamar yadda ya kai ziyara birnin Alkahira da Santanbul.

A yanzu dai ya zama lallai Amurka ta aminta da rashin nasarar da ta samu wajen cimma yunkurin da ta ke yi na wanzar da zaman lafiya a yankin, lamarin da ya taso da ayar tambaya akan irin matsalolin da Amurka ke fuskanta ta fuskar diplomasiyyarta.