Wikileaks ya fitar da wasu bayanai a kan Najeriya

Taswirar Najeriya
Image caption Bayanan da wikileaks ya fitar, ya nuna halin rudanin da aka shiga a Najeriya a dai dai lokacin da marigayi shugaba Umaru Musa Yar'adua ke fama da rashin lafiya.

Wasu takardun da shafin yanar gizo na WikiLeaks din ya fitar da jaridar The Guardian ta Burtaniya ta wallafa, sun bayyana yadda kamfanin mai na Shell a Najeriya ke samun bayanan sirri na gwamnati.

Wani mataimakin shugaban kamfanin a kasashen Afrika Ann Pickard, ya ce kamfanin Shell na samun duk wasu bayanai da yake bukata saboda ma'aikatan kamfanin kan je aiki na wucin gadi a ma'aikatun gwamnati wadanda keda alaka da aikace-aikacen kamfanin na Shell.

An rawaito wasu sakwanni dake cewa ofishin jakadanci Amurka dake Najeriya ya bayyana irin yadda aka shiga cikin wani yanayi na rudani game da ko wanene ke jan ragamar mulki a Najeriyar lokacin da marigayi shugaba Umaru Musa Yar'adua ke fama da rashin lafiya.