Kungiyar Tarayyar Afrika ta dakatar da Cote de Voire

Kungiyar Tarayyar Afurka ta dakatar da kasar Kot de Vuwa daga cikinta, har sai an kyale Alassane Ouattara ya karbi ragamar shugabanci.

Kasashen duniya da dama dai sun amince cewar Mr Ouattara ne ya lashe zaben kasar ta Kot de Vuwa na watan jiya, amma shugaban dake kan karagar mulki Laurent Gbagbo ya kekasa kasa ya ce ba zai sauka ba.

Ramtane Lamamra shi ne kwamishinan Tarayyar Afrika mai kula da harkokin tsaro,ya ce, majalisar ta yanke shawarar dakatar da Kot de vuwa har zuwa lokacin da Mr Alassane Ouattara , mutumin da aka zaba ta hanyar dimokradiyya ya karbi ragamar shugabanci.

A yanzu Mr Gbagbo ba ya fitowa bainar jam'a, yayinda Mr Ouattara ke gudanar da harkokinsa a wani Otel dake da matakan tsaro, yayinda ake fargabar sake barkewar yakin basasa.