Kyautar nobel kan zaman lafiya ga Liu Xiaobo, ba neman cusa dabi'un yammacin duniya a China ba ne

Kwamitin bada kyautar Nobel a kasar Norway ya ce bada kyautar nobel ta zaman lafiya ta bana ga dan kasar Chinar nan mai nuna bijirewa, Liu Xiaobo, ba wani yunkuri ba ne na cusa dabi'un yammacin duniya a China.

Shugaban kwamitin ne Mr Jagland ya bayyana cewar " hakkokin bil adama na duniya, kamar yadda suke kunshe a shelar kasashen duniya, ba wai dabi'u ne na kasashen yammacin duniya".

A gobe ne za a bada kyautar ba tare da Mr liu ya halarta ba.