Ma'aikatar lafiyar Najeriya tayi gargadi akan allurar Chloroquine

Maganin zazzabin cizon sauro na Chloroquine
Image caption Ma'aikatar kiwon lafiya a Najeriya ta gargadi likitocin kasar da su daina yiwa marasa lafiyar da suka kamu da cutar zazzabin cizon sauro allurar chloroquine

Ma'aikatar kiwon lafiya a Najeriya ta umarci likitoci a fadin kasar da su daina yiwa mutanen da suka kamu da zazzabin cizon sauro allurar maganin Chloroquine.

Ma'aikatar lafiyar dai ta ce wani bincike da aka gudanar ya tabbatar da cewa maganin baida tasiri sosai wajen magance cutar.

Ma'aikatar tace tun a shekarar 2004 gwamnati ta hana amfani da maganin na Chloroquine, a don haka ta ce wajibi ne a fara amfani da wannan doka

Dr. Kabir Aliyu Muhammad shine shugaban shirin yaki da zazzabin cizon sauro dake samun tallafin bankin duniya, ya kuma shaidawa BBC cewar yanzu haka likitoci basu cika rubutawa marasa lafiya wannan magani na chloroquine ba.

Ya kuma kara da cewar tuni ake maye gurbin maganin na chloroquine da wani sabon magani da ake kira ACT