China na tsare da masu fafutukar kare hakkin dan adam

Mai fafutukar kare mulkin dumukradiyyar kasar Sin, Liu Xiaobo
Image caption Mutumin da aka shirya baiwa lambar yabon zaman lafiya ta Nobel a kasar Sin, Liu Xiaobo ba zai sami halartar bukin na yau ba, kasancewar yana garkame a gidan yari.

Majalisar dinkin duniya ta ce ta samu labarin cewa hukumomin kasar Sin na tsare da masu fafutukar kare hakkin bil'adama akalla mutum ashirin gabannin bukin bada lambar yabon zaman lafiya ta Nobel a Oslo.

Kujerar da zata kasance babu kowa akanta a wurin bukin ita ce ta mutumin da aka shirya baiwa lambar yabo ta wannan shekarar, mai fafutukar kare dumukradiyya dan kasar Sin Liu Xiaobo, wanda yanzu haka ke zaman gidan yari inda yake fuskantar daurin shekaru goma sha daya.

Wakilin BBC ya ce kasar Sin ta ce kwamitin bada lambar yabon ya zabi wani dake da laifi karkashin dokokin kasar wanda kuma aka yankewa hukunci, don kawai a cimma wata manufa ta wasu kasashen yammacin duniya.

Kasar ta Sin ta kuma yi gargadin cewar duk kasar data halarci bukin bada lambar yabon da za'a gudanar a yau, zata ga abinda zai biyo baya, kodayake bata fayyace irin matakin da zata dauka ba