Shafin Wikileaks ya wallafa bayanan sirri kan Nigeria

Goodluck Jonathan
Image caption Shugaban Nigeria, Goodluck Jonathan

Bayanan da shafin Wikileaks ya wallafa sun ce a lokacin da ya ke mukaddashin Shugaban kasa, Dr Goodluck Jonathan ya shaidawa Jakadiyar Amurka a Nigeria cewar shi ba dan siyasa ba ne, kuma ba shi da kwarewa ta jan ragamar mulki.

Haka nan kuma Dr Goodluck Jonathan ya ce yana kokarin ganin yadda jama'ar arewacin Nigeria zasu saki jiki da shi.

Shafin na Wikileaks ya ruwaito cewar a wata ganawa da Jakadiyar Amurka ta yi da Dr Goodluck Jonathan, mukaddashin shugaban na Nigeria ya ce akwai wani shiri da tsohon shugaban mulkin sojin Nigeria, Abdussalami Abubakar ke yi na kokarin ganin Shugaba Umaru Musa 'Yar'adua yayi murabus.

Shugaba Goodluck Jonathan ya kuma dora alhakin rudanin da aka shiga a Nigeria akan mutane hudu da ke kewaye da 'Yar Adua.

Mutanen da aka ambato su ne Hajiya Turai 'Yar Adua, uwargidan marigayi Shugaba 'Yar'adua da babban mai tsaron lafiyar sa Yusuf Mohammed Tilde da dogarin shugaba 'Yar'adua Mustapha Onoe-dieva da Tanimu Kurfi mai baiwa marigayin shawara kan harkokin tattalin arziki.

Haka kuma ya ambaci Abba Sayyadi Ruma ministan ayyukan noma da Adamu Aleiro ministan birnin Abuja a matsayin wasu masu hana ruwa gudu.

Dr Goodluck Jonathan yace yarda wadannan mutane suna da wata muguwar aniya, tun da yayi imanin cewa 'shugaba 'Yar Adua baya cikin hayyacinsa.

Bayanan na shafin Wikileaks ya ce jakadiyar Amruka ta kuma baiwa mukaddashin shugaba Goodluck shawarar ya nisanta kansa da tsohon shugaban Nigeria Olusegun Obasanjo.