Kamfanin Shell ya ce yana samun bayanan sirri a Nigeria

Shell

Bayanan da shafin Wikileaks ya fitar wanda kuma jaridar The Guardian ta Burtaniya ta wallafa, sun ce Kamfanin Mai na Shell a Nigeria, ya dasa ma'aiakata a muhimman ma'aikatun kasar domin samun bayani.

Mataimakiyar Shugabar Kamfanin Shell a kasashen Africa, Ann Pickard, ta ce kamfanin Shell na samun duk wasu bayanai da yake bukata saboda ma'aikatan kamfanin kan je aiki na wucin gadi a ma'aikatun gwamnati wadanda keda alaka da aikace aikacen kamfanin na Shell.

Bayanan sun ce Jami'ar kamfanin Shell din ta shaidawa Jakadiyar Amurka a Nigeria cewar gwamnatin Nigeria ta manta da cewar kamfanin na Shell yana da ma'aikatu a dukkanin muhimman ma'aikatu na Nigeria.

Kamfanin Shell dai ya musanta wannan zargi, yayin da kuma aka ambato wani mai magana da yawun kamfanin NNPC na Nigeria ya na cewa