Tunawa da ranar kare hakkin Bil Adama a Najeriya

Hakkin Bil- Adama
Image caption Kungiyoyin kare hakkin bil'adama irinsu Amnesty International sun sha wallafa rohotannin dake nuni da yadda 'yan Najeriya ke fama da cin zarafi a hannun jami'an tsaron kasar, zargin da tuni jami'an tsaron suka musanta

Najeriya zata bi sahun sauran takwarorinta na kasashen duniya don tunawa da ranar kare hakkin bil'adama ta kasa da kasa.

Majalisar dinkin duniya dai ta kebe ranar goma ga watan Disamba ne a matsayin ranar yin tarurruka da bukukuwa don jawo hankulan jama'a akan nau'o'in cin zarafin bil'adama dabam dabam da ake fama dasu.

Kungiyoyin kare hakkin bil'adama a Najeriya sun shirya gudanar da gangami da lakcoci akan abinda suka kira cin zarafin bil'adama da ake fama dashi a kasar.

Manyan kungiyoyin kare hakkin bil'adama kamar su Amnesty International da Human Rights Watch, sun sha wallafa rohotannin dake nuni da yadda 'yan kasar ke fama da cin zarafi a hannun jami'an tsaron kasar, zargin da tuni jami'an tsaron Najeriyar suka musanta