Cin hanci da rashawa ya zama ruwan dare

Matsalar cin hanci da rashawa a duniya
Image caption Matsalar cin hanci da rashawa a duniya

Cin hanci da rashawa, matsala ce da tayi kamari a kasashe da dama na duniya, tare da janyo cikas ga yadda ake gudanar da ayyukan al'umma.

Ana zargin manyan jami'an gwamnati da hada baki da kamfanoni ko bankuna domin sace dukiyar da aka ware don raya kasa.

Alal misali, a wani jawabi da ya gabatar a gaban majalisar dokoki ta Amurka, tsohon shugaban hukumar EFCC mai yaki da masu yiwa tattalin arzikin Najeriya ta'annati, Malam Nuhu Ribadu, ya bayyana cewa abinda aka sace a kasar daga 1960 zuwa 1999, ya kai dalar Amurka biliyan 440.

Malam Nuhu Ribadu ya ce, yawan wadannan kudade sun ribanya wadanda aka kashe a gagarumin shirin gina kasahen turai bayan yakin duniya na biyu har sau shida.

Sannan masana na ganin cewa, kudaden da aka yi sama da fadi da su daga 1999, bayan kafuwar mulkin demokradiyya a Najeriyar ya zuwa yanzu, sun ninka wadannan alkalumma da aka ambata.

Sai dai matsalar ba wai ta tsaya ga bangaren hukumomi ba ne kawai, su ma jama'ar gari na yin amfani da damar su wajen aikata cin hanci da rashawar.

Baya ga masu sauraro, bakin da suka shiga cikin shirin sun hada da Alhaji Abdulkadir Balarabe Musa, tsohon gwamnan jihar Kaduna, da Hon. Rabe Nasir, shugaban kwamitin yaki da cin hanci da rashawa a majalisar wakilan Najeriya, da Malam Mamman Wada, sakataren kungiyar Transparency International mai yaki da cin hanci da rashawa a duniya, reshen jamhuriyar Nijar, da Malam Abubakar Othman, mataimaki na musamman ga shugabar hukumar EFCC mai yaki da masu yin zagon kasa ga tattalin arzikin Najeriya.