Bom ya fashe a ofishin 'yan sandan Kandahar

Bom a Kandahar
Image caption Fashewar a Bom a ofishin yan sanda

Wani babban bam ya fashe a kusa da shelkwatar wani caji ofis dake birnin Kandahar a kudancin kasar Afghanistan, inda mutane shida suka jikkata.

Mahukunta sun ce bam din ya fashe ne a inda 'yan sandan ke ajiye motocinsu.

Kawo yanzu babu masaniyar ko an yi amfani ne da wata na'ura wurin tada bam din daga nesa ko kuma dan kunar bakin wake ne ya tada bam din.

A cewar wakilin BBC duk da cewa mutanen da suka jikkata kadan ne, harin bam a kofar ofishin 'yan sandan Afghanistan wani babban abin damuwa ne ga kungiyar kawance ta NATO.