Murar aladu ta kashe mutane goma a Burtaniya

kwayar cutar H1N1
Image caption Cutar murar aladu

Ma'aikatan kiwon lafiya a Burtaniya sun ce cutar murar aladu ta hallaka mutane goma a kasar daga watan Satumba zuwa yanzu.

Hukumar kula da kiwon lafiyar al'umma ta ce gaba daya mutane goman manya ne da shekarunsu ba su kai sittin da biyar ba.

Haka kuma an samu rahotannin barkewar murar a wasu makarantu.

A watan Agusta ne dai hukumar lafiya ta duniya ta ce an kawo karshen annobar murar aladun, fiye da shekara guda bayan da kwayar cutar ta H1N1 ta kewaya duniya tare da hallaka dubunnan mutane.