An cimma matsaya kan sauyin yanayi

taron cancun
Image caption Taron sauyin yanayi

Wakilan dake halartar taron kolin Majalisar Dinkin Duniya kan sauyin yanayi a Mexico sun amince da wasu matakai da aka tsara don shawo kan dumamar yanayi tare da kuma taimakawa kasashe masu fama da talatuci yadda zasu yi maganin tasirin da wadannan matakai zasu haifar.

A karshen taron na tsawon makonni biyu da aka yi a wurin shakatawar nan na Cancun, an amince da kafa wani asusu, wanda za'a duiga amfani da kudadensa domin taimakawa kasashe masu fama da talauci domin bunkasa fasahar da za ta rage fitar da hayaki.

Kasar Bolivia ce kawai ba ta amincewa da yarjejeniyar ba, inda ta ce yarjjeniyar ba ta da karfi, kuma tamkar kunar bakin wake ce idan aka amince da ita.

Bisa ga dukkan alamu, Mexico, wadda ke karbar bakuncin taron ce ta yi dabarar shigar da kalamai cikin yarjejjeniyar karshen da kusan kowa ya amince da ita.

A karshe dai wakilai a wurin taron sun yi ta shewa suna murna a yayin da aka yi shelar cimma yarjejeniya bayan shawarwarin da aka shafe ranar karshe ana yi baji-ba-gani.

A yanzu an amince za'a kafa wani asusu wanda za'a yi amfani da kudaden da za'a tara wajen taimakawa kasashe masu fama da talauci domin kare su daga irin illolin da sauyin yanayi zai haifar da kuma taimaka musu domin samun fasahar da za ta rage fitar da hayaki.

Akwai matakan da aka tanada domin rage sare itace da kuma duba yawan hayakin da kowace kasa ta rage daga cikin abun da ta saba fitarwa.

To saidai, yarjejeniyar ta fito karara ta nuna cewar irin alkawarin da kasashen suka dauka na yawan hayakin da za su rage, ko kadan bai kama kafar abin da ake bukata ba, don haka yarjejeniyar ta yi kira ga kasashe da su kara himma wajen rage yawan hayakin da suke fitarwa, sai dai babu wani tanadi a cikin yarjejeniyar na tilasta musu.

Ga kasashe da dama dai wannan rauni ne, to amma duk da haka abin da aka cimma ya zarta zaton galibin masu sa ido akan wannan taro, kuma a gaskiya ma yarjejeniyar na iya share fagen kaiwa ga kulla wata yarjejeniyar mai inganci a taro na gaba.