An cimma matsaya a taron sauyin yanayi

Taron sauyin yanayi a Cancun
Image caption Akwai alamu dake nuna cewa wakilan kasashen duniya dake halartar taro akan sauyin yanayi a Cancun na kasar Mexico sun cimma matsaya

Akwai alamu dake nuna cewa wakilan kasashen duniya dake halartar taro akan sauyin yanayi a Cancun na kasar Mexico sun cimma matsaya, da zata kaiga cimma yarjejeniya na rage gurbatacciyar iskar da suke fitarwa a nan gaba.

Har yanzu dai kasashen Japan da Rasha sun 'ki amincewa da a ci gaba da rage gurbatacciyar iskar da ake fitarwa, a karkashin yarjejeniyar da aka cimma a baya, duk kuwa da lallami da matsin lamba daga wasu shugabannin kasashen masu tasowa.

Wakilin BBC ya ce yayin da lokacin da aka shirya kammala taron ke wucewa, gwamnatin kasar Mexico wacce ita ce mai masaukin baki, ta fitar da daftarin yarjejeniyar da ake fatan za'a kaiga cimma matsaya akai.