Cutar Polio ta kashe yara 200 a kasar Congo

Rigakafin kamuwa da cutar Polio
Image caption Cutar Polio data bulla a jamhuriyar dumukradiyar Congo tayi sanadiyyar kashe yara dari biyu

Asusun tallafawa kananan yara na Majalisar dinkin duniya wato UNICEF,ya ce cutar Polio data bulla a Jamhuriyar Dumukradiyyar Congo ta yi sanadiyar mutuwar mutane dari biyu.

Kakakin UNICEF Martin Dawes, ya ce kasar na fuskantar annobar cutar ta Polio wacce ta bulla a watan Oktoba, inda ya kara da cewa yanzu haka, cutar wacce tafi shafar matasa na ci gaba da yaduwa cikin gaggawa.

Cutar Polio dai tafi shafar kananan yara ne, inda takan yi sanadiyar shanyewar jiki, yayin da a wasu lokutan ma akan kaiga rasa rai.

Sai dai yanzu ana shirin fara gudanar da rigakafin kamuwa da cutar a duk fadin kasar.